Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (AS) – ABNA - ya habarta cewa: Sojojin Amurka sun sanar da kai hare-hare a kan wuraren radar na Iran a Juruk da tsibirin Qeshm, a jiya Juma'a, suna zargin cewa aikin kariyar kai ne na tsaro.
Cibiyar yada labarai ta CNN ta ce "Iran ta harba jirage marasa matuki da dama zuwa mashigar Hurmuz."
Sojojin Kuwait kuma sun bayyana cewa an ji karar fashe-fashe da daddare, suna bayyana cewa "sakamakon fuskantar tsaron sama ne ga hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuki ne."
A nata bangaren, ma'aikatar cikin gida ta Bahrain ta kunna ƙararrawar faɗakarwa sakamakon hare-haren sama.
Kuma duk da tsagaita wuta tsakanin Iran da Amurka da Pakistan ta yi sulhu tun daga ranar 8 ga Afrilu, 2026, Washington na ci gaba da kai hare-hare a kan Iran a mashigar Hurmuz da sauran wurare. Yayin da sojojin Iran ke mayar da martani ga waɗannan hare-haren.
A jiya, sojojin Iran sun sanar da harba makamai masu linzami na gargadi na "Ghadir" da sabbin jirage marasa matuki masu kai hari na "Shahid Dana" zuwa ga jiragen ruwan Amurka guda biyu da suka ce sun ketare iyaka, suna masu nuna cewa jiragen ruwan Amurka "DDG-103" da "DDG-87" sun bar tekun Oman zuwa tekun Indiya.
Wanda a baya, rundunar sojan ruwa ta Iran ta kai hari ga cibiyar bayar da umarni da kula da ayyukan fagen yaki na Amurka da ke da alhakin ayyukan farmaki na Amurka a kan jiragen ruwan kasuwanci na Iran a tekun Oman, wanda ke kan wani jirgin ruwan yaki na Amurka da ke shirin tunkarar ruwan Iran.
Kuma a ranar 21 ga Mayu da ta gabata, Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta sanar da kafa "yankin ikonta na ruwa" a mashigar Hurmuz.
…………………………………………..
Your Comment